Karamin Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle Bello Matawalle ya bayyana cewa ya taimaki gwamnan Jihar Zamfara mai ci Dauda Lawal Dare a lokacin da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon Kasa ta EFCC ke nemansa ruwa a jallo.

Matawalle ya bayyana haka ne a yau Talata a yayin wata fira da gidan talabijin na Channels.

Karamin Ministan ya ce a baya ya taimakawa gwamna Dare wajen samar masa da fasfo bayan kwace nashi da hukumar EFCC ta yi.

Matawalle ya kara da cewa gwamna Dauda ya kuma roke shi akan ya bashi mukamin hadiminsa domin rubuta takarda ga hukumar shige da fice ta Kasa don ta bashi fasfo dinsa.

Karamin Ministan ya kara da cewa bayan kai’wa hukumar ta shige da fice ta Kasa wato Immagration takarda aka bashi fasfo dinsa, inda ya samu damar wuce Jihar Kebbi zuwa Jamhuriyyar Nijar kafin daga bisani kuma ya tsallake zuwa Kasar Birtaniya.

Matawalle ya kara da cewa bayan watanni biyu da suka gabata hukumar EFCC ta aiko da takarda kan cewa suna binciken Dauda amma ya samu zarafin samun fasfo daga gwamantinsa ya tsere.

Matawalle ya bayyana cewa ko kadan bai damu ba da zarge-zargen da gwamna Dare ya ki yi masa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: