‘Yar takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a Jihar Adamawa Sanata Aisha Dahiru Ahmad Binani ta bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a garin Maidugurin Jihar Borno.

Sanata Binani ta bayar da tallafin ne a yau Talata a yayin wata ziyara da ta kaiwa gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum.

A yayin ziyarar Binani ta ce garin Maiduguri gida ne gareta, kuma tana da alaka da garin da tare da buƙatar nuna goyon baya ga jama’ar Jihar ta Borno.

Sanata Binani ta kuma yi addau’ar neman kariya daga sake fadawa cikin wannan hali na iftila’in Ambaliya nan gaba.

Binani ta kuma yi addu’a nema rahma ga wadanda suka rasa rayukansu a yayin ambaliyar ruwan.

Bayan mika tallafani Gwamna Babagana Zulum mika godiyarsa gareta bisa namijin kokarin da ta yi na kai ziyara Jihar, duk da rashin kyawun yanayi da aka samu.

A yau Talata ne dai aka cika kwanaki 14 da fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a Jihar ta Borno wadda ta haifar da manyan a sarori, da lalata gidaje, da gonaki, da kuma rasa rayukan mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: