Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa a shirye ta ke wajen fuskantar tsohon gwamnan Jihar Kogi Bello Yahaya a gaban kotu.

Mai magana da yawun hukumar , Dele Oyewale ne ya bayyana hakan,ya ce dole sai Yahaya Bello ya fuskanci alkali kan zargin da ake yi masa na aikata badakala.
EFCC ta ce kamar yadda a baya aka gurfanar da tsofaffin gwamnoni, ministoci, da manyan jami’an gwamnati kan zargin almundahana, ya zama wajibi Yahaya Bello shima ya gurfana a gaban kotu.

Hukumar ta ce tun da tsohon gwamnan na Kogi ya ki mutunta gayyatar da hukumar ta sha yi masa a baya, yaje gaban kotu yayi jawabi a gaban Alkali.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa tuni ta kammala hada kwararan shaidu kan zargin da ake yi wa , Yahaya Bello.
Dele ya ce da zarar an fara zaman shari’ar Yahaya Bello, za a zakulo shaidun da aka tara sannu a hankali domin bayar da shaida akan zargin da ake yi masa.