Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ta gabatarwa da wata Babbar Kotu a birnin tarayya Abuja sabbin tuhume-tuhume 16 da suka shafi badakala da ake yiwa tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Zarge-zargen da hukumar ta gabatarwa da kotun ta hannun lauyoyinta Kemi Pinheiro da Rotimi Oyedepo da sauran wasu lauyoyi bakwai ne suka shigar da tuhume-tuhumen.
Bayan Yahya Bello hukumar ta kuma gabatarwa da kotun Umar Shuaibu Oricha, da Abdulsalam Hudu a matsayin karin waɗanda ake zargi da aikata badakalar tare da Yahya Bello.

Hukumar ta EFCC na dai zargin Yahya Bello ne da yin sama da fadi da fiye da naira biliyan 80 a lokacin da ya ke kan kujerar gwamnan Jihar.
