Gwamnan Jihar Anambra Chukwuma Soludo, ya ce gwamnatinsa ta shirya tsaf domin fara biyan ma’aikata sabon mafi karancin albashi na naira 70,000.

Gwamnan Soludo ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a cibiyar bunkasa mata ta Farfesa Dora Akunyili da ke Awka a Jihar a yayin wani taro, da ya gudanar da shugabanni makarantun firamare da sakandare na gwamnatin jihar.
Gwamnan ya ce daga sabon watannan na Oktoba mai kamawa gwamnatin za ta fara biyan ma’aikatan sabon mafi karancin albashin.

Gwamnan ya bayyana cewa daga mako mai zuwa za a samar da tsarin ilimi kyauta ga manyan dalibai a Jihar na dukkan makarantun gwamnati a Jihar.

Gwamna Sulodo ya kuma bayar da umarnin mayarwa da daliban da suka biya Naira 5,000 a wannan zangon karatun kudinsu.