Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta karbo bashin Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Raya cigaban kasar Faransa wato French Development Agency domin gina sabbin matatun ruwa na Tamburawa da kuma inganta samar da ruwan sha a Jihar.

Gwamna Abba ne ya bayyana hakan a yayin wani taron ƙarawa juna sani na kwanaki biyu domin bitar ayyuka wanda aka gudanar a Kano.
A yayin taron gwamnan ya samu wakilcin Kwamishinan Ruwa na jihar Alhaji Ali Haruna Makoɗa.
Taron ya kuma samu halartar wakilai daga Jihohin Filato Enugu da Kuma Ondo.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa aikin samar da ruwan na da manufar inganta hanyoyin samar da ruwan sha na Kasa, wanda kuma ya samu amincewa daga Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Najeriya.

Gwamnan ya kara da cewa a baya an samu tsaiko ne akan aikin bisa annobar cutar Korona wata COVID-19 da kuma sauran wasu kalubale da aka samu, inda ya ce a halin yanzu su na sanya ran kammala shi nan da shekaru biyu masu zuwa.
Manajan Daraktan hukumar ruwa ta Jihar Kano injiniya Garba Ahmad Bichi ya tabbatar da cewa aikin ya hada da gina sabuwar ma’adanar ruwa mai cin lita miliyan 250 a kowace rana, wanda kuma zai magance matsalar karancin ruwan da ake fama da shi a Jihar bisa yawaitar al’ummar da ake ci gaba da samu a fadin Jihar.