Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ta haramta yin noma akan hanyoyin shanu da filayen kiwo na Jihar daga karshen daminar nan ta bana.

Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Abdullahi Garba Faskari ne ya bayyana haka a yayin wata ziyara da ya kai ƙananan hukumomin Mai’adua da Zango a Jihar domin duba halin gonaki ke ciki.
Sakataren ya bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin kawo karshen saɓanin da ke haifar da rikici a tsakanin manoma da makiyaya.

Faskari ya ce ya kai ziyara ne bayan samun wasu rahotanni daga makiyaya cewa manoma sun yi noma akan hanyar da suke wucewa da shanu a wasu ƙananan hukumomin Jihar.

Ya ce gwamnati Jihar ta gudanar da zama da manoma da kuma makiyaya da abin ya shafa akan lamarin musamman dangane da wata hanya da ta tafi har zuwa Jamhuriyar Nijar.
Sakataren ya kara da cewa zaman ya gudana ne tare da shugabannin kananan hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da hakikanin lamarin.
Daga cikin Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da, Mashi, Kaita, Dutsin-Ma, Mai’adua da kuma Zango.
Faskari ya tabbatar da cewa daga yanzu an hana manoma yin noma akan hanyoyi da guraren da shanu ke wucewa da filayen kiwo a fadin Jihar.