Babbar kotun tarayya da ke zamnata a Jihar Kano ta yi watsi da buƙatar Jam’iyyar APC da ta shigar gabanta dangane da zaben Kananan hukumomin Jihar da ke tafe.

Karar da jam’iyyar ta APC ta shigar gaban kotun na neman kotun da ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar KANSIEC daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Jihar da za a yi a ranar 26 ga Oktoba mai kamawa.

Aminu Aliyu-Tiga da jam’iyyar APC ta hannun lauyansu barista Mustapha Idris ne suka shigar da karar tun a ranar 18 ga watan Satumban da muke ciki tare kuma da gabatar da ita a gaban kotun a ranar 20 ga watan Satumba.

Karar wanda aka shigar da ita gaban Alkalin kotun Mai Shari’a Simon Amobeda, inda suke neman kotu da ta hana hukumar zabe ta Jihar gudanar da zaben na kananan hukumomin, tare da bayar da umarni ga dukkanin ɓangarorin da su bar abubuwa a yadda suke.

Daga cikin wadanda jam’iyyar ta APC ta ke kara, sun hada da hukumar zaben, majalisar dokokin Jihar Kano, kwamishinan shari’a na Jihar, da sauran wasu mutane.

Daga karshe Alkalin kotun ya kuma ɗage sauraron shari’ar har zuwa ranar 4 ga watan Oktoban shekarar nan domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Inda kuma ya gargadi bangarorin da su gujewa dukkan wani mataki da zai hana sauraron karar da kuma gaggauta yanke hukunci akanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: