Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC reshen jihar Akwa Ibom ta tsunduma yajin aiki a fadin jihar.

Ƙungiyar ta kuma umarci dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar da su dakatar da gudanar da ayyukansu a yau Alhamis domin shiga yajin aikin.

Rahotannin sun bayyana cewa kungiyar ta shiga yajin aikin ne saboda wahalar da ma’aikata ke sha sakamakon tashin farashin man fetur wanda kudinsa ya kai Naira 2,500 akan kowace lita guda.

Gwamnan jihar ya yi alƙawarin shiga tsakani kan lamarin, tare da gargaɗin ɗaukar mataki kan masu sayar da man fetur fiye da farashinsa na kasuwa.

Sai dai shugaban Kungiyar na jihar, Kwamared Sunny James ya nuna takaicinsa kan cewa duk da alƙawarin da gwamnan ya daukar musu har yanzu babu abin da ya sauya yayin da mutane ke ci gaba da shan baƙar wuya.

Sunny ya ce hakan ne ya sanya kungiyar ta kira taron gaggawa da shugabanninta, inda kuma bayan kammala taron suka cimma matsayar tsunduma yajin aikin a yau.

Acewarsa wahalhalun da ma’aikata ke shane ya sanya suka dauki matakin shiga yajin aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: