Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da ake neman wasu biyun sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a ranar Talata wanda ya haifar da ambaliya a wasu sassan garin Ibadan na jihar Oyo.

Odineto Hukumar na shiyyar Kudu maso Yamma Olanrewaju Kadiri, ya bayyana cewa ambaliyar ta yi sanadiyyar rushewar wasu gidaje da shaguna da kadarori na miliyoyin kudi a jIhar.
Acewarsa a halin yanzu hukumar da hadin giwar ƙungiyar Red Cross suna kan aikin kai ziyara unguwannin da lamarin ya shafa domin kididdige irin barnar da ambaliyar ta haifar.

Rahotannin sun bayyana cewa ambaliyar ta shafi yankin Karamar Hukumar Ibadan ta Yamma inda aka shafe tsawon a wanni biyar ana yin ruwa a yankin.

Hukumar ta ce a halin yanzu tana ci gaba da ganin al’amura sun daidaita a yankin.