Tsohon gwamnan jigar Kogi Yahaya Bello ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya shiga tsakani a rikicinsa da hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Daraktan ofishin tsohon gwamnan kan yada labarai Ohiare Michael ne bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa EFCC nada wata mummunar manufa akan Yahya Bello.

tsohon gwamna na Kogi ya zargin hukumar ta EFCC na kokarin ganin ta ci amanarsa a idon duniya.

Sanarwar ta buƙaci shugaba Tinubu da ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin domin bankado ainihin dalilan EFCC na matsawa Yahaya Bello.

Michael ya kara da cewa Yahya Bello bai aikata laifin komai ba har sai kotu ta tabbatar da laifinsa, inda ya ce a halin yanzu zarg-zargen da EFCC ke yiwa Yahya Bello ba su da tushe belle makamai.

Wannan dambarwa da taki ci taki cinyewa tsakanin Yahya Bello da EFCC, na faruwa ne sakamakon zarginsa yin badakalar sama da naira biliyan 80 da kuma sauran wasu lallafuffak a lokacin da yana kan kujerar gwamnan Jihar, inda ya ke ta tserewa hukumar a yunkurin da ta ke yi na kamashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: