Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoma shida a lokacin da suke tsaka da aiki a cikin gonakinsu a Jihar Kaduna.

Wadanda maharan suka sace sun kasance hudu maza biyu mata a ƙauyen Gidan Busa da ke cikin ƙaramar hukumar Kachia ta Jihar .
Wani shugaban al’ummar yankin da ya tabbatarwa da Jaridar Daily Trust faruwar lamarin a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Litinin din da ta gabata.

Shugaban Al’ummar ya ce maharan sun je gonakin mutanen ne ɗauke da makamai, inda suka far musu su na tsaka da aiki.

Acewarsa bayan faruwar lamarin ya sanar da wasu jami’an Sa-kai da ke ƙauyen Jobgwom wanda ke makwabtaka da su, inda suka nufi zuwa cikin dajin da maharan suka tsere da mutanen.
Kazalika ya ce a ranar ta Litinin din ne wasu ƴan bindiga suka kai hari a wata rugar Fulani a Gadan-Malam Mamman da ke makwabtaka da kauyen nasu na gidan Busa inda suka sace wasu shanu.
Ya ce ƴan bindigan da suka kewaye ƙauyen ɗauke da makamai, sun harbe wasu mutanen ƙauyen biyu tare da raunata su, a lokacin da suke tserewa da shanun da suka sace.