Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Talata 1 gawatan Oktoba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata.

Ministan harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji Ojo ne ya sanar da haka a madadin gwamnatin tarayya.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren din din din a ma’aikatar, ta buƙaci ƴan Najeriya dasu ƙara haƙuri da jajircewa domin hakan ba zai tafi a banza ba.

Sannan ya bukaci hadin kai tare da cewar, ba za a taba samun nasara ba sai an samu haɗin kai daga ƴan ƙasar baki daya.

Haka kuma ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da aikin da zai kai ƙasar zuwa gaba.
A kowacce ranar 1 ga watan Oktoban kowacce shekara ne ake bikin tunawa da samun ƴancin kai a Najeriya, wanda a bana ta cika shekara 64.