Jami’an tsaron hadin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda da DSS, NSCDC da kuma na sa-kai na Jihar ta Katsina KSWC sun samu nasarar kubtar da wasu manoma Mata shida da ‘ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da su tun a ranar 26 ga watan Satumban nan a kusa da Kauyen Gurbin Magarya da ke cikin karamar hukumar Jibia a Jihar.
Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na Jihar Dr Nasir Mu’azu ne ya tabbatar da nasarar da jami’an suka samu, tare kuma da jinjina musu da bisa namijin koƙarin da jami’an tsaron suka yi.

Ya ce Bayan sace mutanen jami’an sun kai daukin wajen kubtar da mutanen, da ‘yan bindigar suka sace.

Daga cikin manoman da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su sun kasance mata uku, yara uku a lokacin da suke girbe masara a cikin karamar hukumar.