Akalla gidaje 329,000 ne su ka rushe yayin da gonaki da dama su ka lalace sanadin ambaliyar ruwa a jihar Kebbi.

Amfanin gona kamar shinkafa, gero, wake da sauran kayan abinci ne su ka lalace sanadin ambaliyar ruwan.
Haka kuma mutane 29 ne su ka mutu a sanadin ambaliyar ruwan sama.

Kwamishinan noma a jihar Yakubu Birnin Kebbi ne ya tabbatar da haka yayin da yake yin bayani dangane da adadin asarar da aka yi.

Ya ce lamarin ya sha kan gwamnatin jihar don ganin an ragewa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗi.
A sakamakon haka su ka yi kira ga gwamnan tarayya da ta kai musu ɗauki.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta samar da iri da kayan aikin noma ga manoma, sai dai har yanzu akwai buƙatar ƙari.
Sannan ya nuna damuwa a kn halin ko in kula da wakilai a zauren majalisar wakilai da dattawa ba su yi wata hobbasa a kan lamarin ba.