Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunayen mutane Tara gaban Majalisar Dattawan Kasar domin tantancesu da kuma amincewa da nadinsu a matsayin shugabannin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yammacin Kasar.

Mai magana da yawun shugaban na Musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a yau Asabar.
Bayo ya ce nadin na zuwa ne bayan sanya hannun da shugaba Tinubu ya yi akan dokar samar da sabuwar hukumar tun a ranar 24 ga watan Yulin da ya gabata.

Daga cikin wadanda shugaban ya nada sun hada da Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji a matayin shugaban hukumar wanda ya fito daga Jihar Kano, Sai kuma Ambassado Haruna Ginsau da ya fito daga Jihar Jigawa zai rike mukamin shugaban Majalisar gudanarwar hukumar.

Sauran sun hada da Dr Yahya Umar Namahe daga Jihar Sokoto, Aminu Sulaima daga Jihar Kebbi, Tijjani Yahya Kaura daga Jihar Zamfara, Abdulkadir Usman daga Jihar Kaduna, Injiniya Muhammad Ali Wudil daga Jihar Kano, Nasidi Ali daga Jihar Jigawa, da kuma Shamsu Sule daga Jihar Katsina.
Ana sanya ran sabuwar hukumar za ta fara aiki nan bada jimawa ba, inda hukumar za ta mayar da hankali wajen samar da ci gaba bunƙasa tattalin arziki da kuma kyautata al’umma a yankin.
Sanarwar ta kuma ce ana kyautata zaton sabbin shugabannin da aka nada za su yi aiki da ƙwarewar da suke da ita wajen bunkasa sabuwar hukumar ta yankin Arewa maso Yamma.