Shugaban jam’iyyar APC na Kasa kuma Tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa Masarautar Bichi a gurinsa masarauta ce da sarki mai daraja ta daya a cikinta.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yau Asabar, a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai karamar hukumar bayan rasuwar wasu jami’an ‘yan sanda a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Jihar Edo.
A yayin ziyarar Ganduje ya nuna rashin jindadinsa akan mutuwar jami’an ‘yan sanda a lokacin da suke dawowa daga zaben gwamnan Jihar Edo.

A ziyarar ta Ganduje ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 20 ga ‘yan uwa da iyalan jami’an da suka rasa rayukansu a yayi hadarin.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma mika sakon ta’aziyyar ga babban sufetan yan sanda na Kasa da kuma jihar Kano da iyalan wadanda suka mutu.
A jawabin na Ganduje ya ce masarautar Bichi tana da sarki mai daraja ta daya ne a cikinta.