Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya mika sakon jaje ga yan kasuwar Kantin Kwari da al’ummar Jihar bisa iftila’in tashin gobara da aka samu a cikin Kasuwar.

Gwamnan ya mika sakon jajen ne ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook a jiya Lahadi.
Gwamnan ya kuma nuna rashin jindadinsa bisa tashin gobarar da aka samu a cikin Kasuwar a gidan Inuwa Mai Mai, wanda ta kone shaguna masu tarin yawa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa shima ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa, gwamna ya ce gobarar da aka samu a cikin Kasuwar, hakan zai yi matukar kawo babban nakasu ga tattalin arzikin Jihar.

Dawakin Tofa ya ce a sarar da aka samu a cikin Kasuwar ba iya ga ‘yan Kasuwar kadai ya shufa ba, harma da al’ummar Jihar baki daya.
Gwamnan ya kuma bukaci da ‘yan Kasuwar da su kara lura sosai domin ganin an gujewa dukkan wani abu da ka iya kara haifar da hakan a nan gaba.
Gwamnan ya kuma yaba da irin kokarin da hukumar kashe gobara ta yi da sauran wadanda suka taimaka wajen samun nasarar kashe wutar.
Sannan yayi kira ga masu ruwa da tsaki na kasuwar da su mayar da hankali wajen kiyaye matakan kariya domin hana faruwar irin haka a nan gaba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafawa tare da nuna goyon baya ga ’yan kasuwar da abin ya shafa.