Gwamnan Jihar Kogi Usman Ododo ya amince da Naira 72,500 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Jihar da kuma ƙananan hukumomi.

Gwamna Ododo ya amince da biyan sabon mafi karancin albashin ne a yau Litinin, bayan karɓar rahoton kwamitin da gwamnatin ta kafa kan mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Jihar.
Gwamnan ya ce za kuma ayiwa ma’aimatan Jihar sauye-sauye, wanda hakan na daga cikin cika alƙawarin da gwamnatinsa ta yiwa al’ummar Jihar a lokacin yakin neman zabe.

Ododo ya kuma bayyana dakatar da cire haraji ga dukkan ma’aikatan gwamnatin Jihar har na tsawon shekara daya.

Gwamnan ya bukaci ma’aikatan gwamnatin da su goyi bayan dukkan manufofin gwamnatinsa na kawo canje-canje a fadin Jihar.
Gwamna Usman Ododo ya kara da cewa daga wannan watan na Oktoba za a fara biyan ma’aikatan mafi karancin albashin.
Shugaban Kwamitin kan Mafi ƙarancin Albashi kuma shugaban ma’aikata na Jihar Mista Elijah Abenemi ya ce an kafa kwamitin ne tun a ranar 17 ga watan Satumban da ya kare.
Shugaban ya ce kwamitin ya gudanar da aikin tantancewa tare da yadda za a fara biyan ma’aikata mafi karancin albashin.