Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ta bayyana rashin jindadinta bisa koma bayan da ta ke samu a cikin ayyukanta.

Shugaban hukumar na Kasa Ola Olukayede ne ya bayyana hakan ne a yau Litinin a Abuja a yayin wani taron karawa juna sani ga alkalai karo na shida wanda aka gudanar a dakin taro na cibiyar shari’a ta kasa birnin.
Shugaban ya ce daga cikin nakasun da hukumar tasu ta samu a cikin ayyukanta sun hada da haramta gudanar da bincike a wasu jihohi 10 na Kasar da ba za ta yi ba, sakamakon kotu da ta haramta mata gudanar da binciken.

Taron wanda aka yi masa take da Hada kan masu ruwa da tsaki wajen yaki da cin hanci da rashawa, shugaban bai bayyana Jihohin da Kotu ta haramtawa hukumar bincika ba.

Shugaban ya kuma koka bisa yadda ayyukan hukumar ke ci gaba da fuskantar koma baya, bisa hukuncin kotun da ya sanyawa hukumar.
Kazalika ya kara da cewa daga cikin kalubalen da hukumar ta su ke fuskantar ciki harda yadda kotuna ke dage shari’o’in manyan laifuffuka da hana hukumar kama masu laifi da dai sauransu.
Acewarsa akwai bukatar kotuna da su daina yawaita bai’wa mutanen da ake zargi takardar umarnin hana hukumar kama su a dukkan lokacin da bincike yazo kansu.
Sannan ya ce hukumar za ta gyara kura-kuranta, tare da daukar matakan gyara tsarin binciken hukumar kamar yadda dokar Kasar ta tanada.