Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta tabbatar da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour Party ta Kasa.

A zaman yanke hukuncin da Kotun ta yi a yau Talata,Alƙalin kotun mai shari’a Emeka Nwite, ya tabbatar da shugabancin Abure da taron jam’iyyar da aka yi a watan Maris din 2024 wanda ya kafa shugabancin jam’iyyar.
Sannan Alkalin kotun ya umarci hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da ta amince da Abure a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar, duk da cewa hukumar ba ta amince da shugabancin ba.

A baya hukumar ta INEC ta bayyana cewa taron jam’iyyar ta LP da aka gudanar a Jihar Anambra, an yi shi ne ba bisa ka’ida ba, kuma ta ce wa’adin Abure zai ƙare a watan Yunin shekarar nan.

Hakan ya sanya wasu ’ya’yan jam’iyyar da suka hada da ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi da Gwamna Alex Otti gudanar da taro, tare da naɗa Misis Nenadi Usman a matsayin shugabar kwamitin kulawa da za ta warware matsalolin jam’iyyar.
Sai dai tsagin Abure ya kira taron gaggawa da kuma ƙin amincewa da naɗin nata.
Bayan kammala hukuncin kotun Abure ya nuna jindadinsa bisa nasarar da ya samu a kotun.