Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ne ya kassara Najeriya wanda hakan ya hana ta cigaba.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a taron da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta shirya da hadin gwiwar cibiyar nazarin shari’a ta kasa ga alkalai wanda aka gudanar a Abuja a jiya.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kasim Sheettima, inda ya bayyana taikacinsa dangane da yadda ake ci gaba da fuskantar cin hanci da rashawa a fadin Kasar.

A yayin taron shugaba Tinubu ya ce a shirye gwamnatinsa ta ke wajen kawar da rashawa da ta ki ci taki cinywa a fadin Kasar.

Shugaban ya kara da cewa dabi’ar cin hanci da rashawa ta ratsa dukkanin sassan Kasar kuma ta shafi kowane dan kasa, lamarin da ya kara munana al’amura.

Acewarsa ya zama dole sai kowane dan kasa ya yi hobbasa wajen ganin an kawo karshen cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa yaki da rashawa ba aikin hukumomin yakar cin hanci da rashawa kadai ba ne, su ma yan kasa suna da rawar da za su iya taimakawa wajen yaki da mummunar dabi’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: