Gwamnan jihar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya bayar da umarnin kara daukan mataki domin cigaba da kawar da masu garkuwa da mutane a Jihar.

Radda ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai sansanin horas da jami’an tsaron sa-kai a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan Ibrahim Kaula ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook a jiya Litinin.

Kaula ya ce gwamna Radda ya bayyana kudurin daukar jami’an sa-kai 500 domin ba su horo na musamman don cigaba da yaki da ‘yan bindigan da suka addabi Jihar.

Sanarwar ta ce za a dauki jami’an na sa-kan ne daga kananan hukumomi goma da suke fama da matsalar yan bindiga a jihar.

A yayin bayar da horan Radda ya kai ziyarar gani da ido kan yadda horon yake gudana, tare da ba su kyautar Naira miliyan 5.

Gwamna Dikko ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawo karshen batagari a Jihar, inda ya ce a halin yanzu an tanadi dukkan kayan aiki na jami’an sa-kan da za su bukata a yayin gudanar da aiki.

Radda ya ce daga cikin abubun da aka tanadar musu sun hada da motoci, babura, makamai da kudin alawus da za a rika ba su domin tabbatar da ganin an kawo karshen yan bindiga.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: