Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya mika sakon ta ya murnarsa ga gwamna Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa samun lambar yabo da yayi daga kungiyar MalamaI ta Kasa wato NUT.

A wallafar da yayi a shafinsa na X, Sanata Kwankwaso ya jinjinwa gwamna Abba bisa jajircewarsa wajen farfado da harkar ilimi a Jihar.

Kwankwaso yayi kira gareshi da ya kara jajircewa, akan gyaran da ya ke yi a fannin ilmi, domin ganin ya cimma dukkan manyan manufofin da ya sanya a gaba wajen gyaran ilimin Jihar.

An dai karrama gwamna Abba da lambar yabon ne a yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2024 wanda aka gudanar a filin Eagle Square da ke birnin Abuja.

Bikin wanda ya samu halartar malamai da shugabanni bangaren ilimi daga gurare daban-daban na Kasar, domin karrama manyan nasarorin da ɓangaren ilimi ya samu a Najeriya.

Ƙungiyar NUT ta karrama gwamna Abba ne domin ganin ya kara inganta harkar ilimi a fadin Jihar ta Kano, bayan durkushewar da yayi a baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: