Majalisar Dattawan ta Kasa ta maince da naɗin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin sabon shugaban hukumar jindadin alhazai ta Kasa NAHCON.

Majalisar ta amince da zaman nadin na shi ne a zaman da ta gudanar a yau Talata.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Pakistan ne tun a ranar 19 ga watan Agusta, bayan sauke shugaban hukumar Jalal Arabi daga mukaminsa bayan zarginsa da yin sama da fadi da wasu kudade a yayin aikin hajjin bana da ya gabata.

Kafin naɗin Pakistan a matsayin shugaban hukumar ta NAHCON ta Kasa a baya ya rike shugabanci hukumar ta Jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: