Malaman Makarantun Firamare na Babban Birnin Tarayya da ke karƙashin Ƙungiyar Malamai ta Kasa NUT sun janye daga yajin aikin da suka shiga tun a ranar 18 ga watan Satumba.

Kungiyar ta janye daga yajin aikin ne a jiya Litinin bayan wani taron gaggawa da suka yi a garin Gwagwalada.
A yayin tafiya yajin aikin kungiyar ta umarci malamai daga kananan hukumomi shida na birnin da su shiga yajin aikin, sakamakon rashin biyan ragowar kashi 60 na albashin watanni 25, da kuma rashin aiwatar da biyan ragowar kashi 40 na alawus na musamman, da sauran wasu haƙƙoƙinsu.

A sanarwar da mai magana da yawun kungiyar Abdullahi Mohammed Shafas ya fitar, ya ce sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi musu alƙawarin biya buƙatun malaman.

Ministan ya yi alƙawarin fara biyan ragowar kashi 60 na albashinsu.
Sannan Wike ya kuma umarci ofishin ajiyar kuɗin na Abuja da su yi amfani da kashi 1p na kuɗin shiga da ƙananan hukumomi suka tara don biyan malaman.
Shafas, ya kuma ce ƙungiyar ta yi la’akari da jajircewar ministan wajen biyan sauran buƙatun malaman, wanda hakan ya sa suka dakatar da yajin aikin.
Kungiyar ta KUMA roƙi Wike da ya gaggauta ɗaukar mataki akan sauran bukatunsu, kamar biyan alawus ɗin kashi 40, alawus na Naira 35,000, da ƙarin albashi na kashi 25 da 35 da bayan an biya su ragowar kuɗaɗen da suke bi.