Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta samu nasarar kubtar da wasu mutane da ‘yan bindiga suka yi yunkurin yin garkuwa da su a wasu daga cikin ƙananan hukumomi biyu na Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Abubakar Sadi Aliyu ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:00 na rana daga ƙauyen Matarau da ke cikin karamar hukumar Dan Musa a Jihar.
Kakakin ya ce maharan sun yi yunkurin yin garkuwa ne da wasu mata a cikin karamar hukumar, inda kuma bayan samu kiran gaggawa jami’an su yi nasarar kubtar da mutanen.

Har ila yau ya ce a karamar hukumar Faskari kuwa, jami’an ne suka sake samun kiran gaggawa a jiya Litinin da misalin karfe 2:30 na rana, kan cewa yan bindigar sun tare hanyar ƙauyen Unguwar Kafa, inda kuma suke yunkurin garkuwa da wasu mata da kanana yara, anan ma jami’an suka sake samun nasara akan maharan.

Sadik ya kara da cewa jami’an nasu sun kuma ceto mutane Takwas wadanda maharan suka yi yunkurin sacewa.
Kakakin ya ce bayan musayar wutar da jami’an nasu suka yi maharan sun tsere dauke da raunuka a tare da su.