Gwamnan Jihar Adamawa Ahmad Umar Fintiri ya bayyana cewa baya goyan bayan soke hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC a Kasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a gidana Talabijin na Channels a cikin shirinsu na ‘Hard Copy’.
Fintiri ya ce babu wani alfanu matukar aka soke hukumar, kamata yayi a kara karfafa ayyukan hukumar na ganin ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata.

Gwamna Fintiri ya kara da cewa a halin yanzu ba lokaci wanda ya kamata a soke hukumar ba, ko da kuwa an samar da ita ne ta hanyar doka ko akasin haka, kawai abinda ya fi bukatuwa hukumar ta yi aikinta yadda ya kamata.

Gwamnan na wannan kalami ne biyo bayan wata ƙarar da gwamnonin Jihohi 16 na Kasar suka shigar da hukumar kara gaban Kotun Ƙoli, tare da ƙalubalantar ingancin dokar da ta kafa hukumar.