Gwamnan jihar Taraba Abgu Kefas ya ce gwamnatin jihar ba ta da shirin rushe babban masallacin garin da kuma fadar masarauta.

Gwamnan jihar ya bayyana haka ne bayan da aka zargi gwamnatin da yunkurin rushewa.

Kwamishiniyar yada labarai a jihar Zainab Usman ce ta musanta batun tare da cewar labarin ba shi da tushe balle makama.

Ta ce irin wadannan labarai na kawo hargitsi da rudani a cikin al’umma.

A cewarta, gwamnatinsu ta himmatu ne wajen samar da abubuwa masu ma’ana ba tare da nuna bambancin addini ko harshe ba.

Sannan gwamnatin na iya kokarinta don tabbatar da zaman lafiya, adalci da jin dadi a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: