Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun hallaka mutane biyar a jihar Filato.

An kai harin wasu yankuna a karamar hukumar Bokkos ta jihar.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da shugaban kungiyar ci gaban Bokkos da sakataren sa su ka sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce an kai harin ne a ranar Litinin.

Maharan sun kai harin a ƙauyukan Rafut, da ke ƙarƙashin Kwatas da ƙarfe 07:00pm na dare.
Sanarwar ta ce huɗu daga cikin waɗanda aka hallaka matasa ne sai kuma wani tsoho guda.
Shugaban ya ce a ranakun 7, da 10, 11, da 12 na watan Oktoba an kai hare-haren da su ka yi silar rasa rayuwar mutane da dama.
Sai dai sun ce tuni su ka sanarwa da mahukunta halin da ake ciki.