Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya amince da naira 75,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan Jihar.

Gwamna Nasir ya amince da biyan mafi karancin albashin ne ta cikin wata sanarwa a shafin gwamnatin Jihar na X ta tabbatar da hakan bayan sanya hannun a kan dokar a yau Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya sanya hannu akan dokar ne a lokacin wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar da ‘yan kungiyar kwadago.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: