Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Ogun ta bayyana cewa ta ware sama da naira biliyan Biyu domin gudanar da zaben Kananan hukumomin Jihar da ke tafe.

Shugaban hukumar zaben Jihar Babatunde Osibodu ya tabbatar da hakan, inda ya ce sun ware kudaden ne domin ganin an gudanar da muhimman ayyuka da za su taimaka wajen ganin an yi zaben cikin nasara.
Shugaban ya bayyana cewa za a kashe kudaden ne domin yin zirga-zirga a lokacin zaben wanda za a gudanar a ranar 16 ga Nuwamba mai kamawa.

Shugaban ya kara da cewa za a karbo kayayyakin zaben daga hukumar zabe ta Kasa INEC akan kudi Naira miliyan 200.

Babatunde ya ce ware kudin ya samo asali ne bisa tsadar kayayyakin zabe da kudin mota sakamakon hauhawar farashi da kuma tsadar man fetur.
Acewarsa a shekarar 2021 da ta gabata an buga rajistar zabe daga hukumar INEC ta Kasa akan kudi Naira miliyan 15, inda a yanzu kuma za a yi rijistar akan kudi Naira miliyan 200.