Gwamnan Jihar Benue Alia ya dakatar da kwamishinan shari’a na Jihar, sakamakon shiga korafe-korafe akan dokar da ta kafa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC a Kasar.

Mai magana da yawun gwamnan Kula Tersoo ne ya tabbatar da dakatar da kwamishinan a tattaunawa da jaridar Punch a jiya Laraba.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnan ya dakatar da kwamishinan ne sakamakon shiga shari’ar da ya yi ba tare da neman izinin gwamnan ba.

Hakan ya biyo bayan shigar da korafi a Kotun Koli da wasu jihohi 16 suka yi akan dokar da samar da hukumar ta EFCC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: