Babbar Kotun Jihar Kano ta sanya ranar 20 ga watan Nuwamba mai kamawa a matsayin ranar da za ta yanke hukunci akan tsohon gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa Hafsa Ganduje, da karin wasu mutane, bisa zargin da ake yi masu da aikata badakalar kudade a Jihar.

Kotun ta sanya ranar yanke hukuncin ne a zaman da ta gudanar a jiya Laraba.

Kotun ta ce za ta saurari korafe-korafen ne daga wasu mutane shida kan zargin badakalar da ake yiwa Ganduje da mukarrabansa, kan laifuffuka takwas.

Lauyan wadanda ake kara Adeola Adedipe ya bayyana cewa a shirye suke domin cigaba da shari’ar da ake yi musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: