Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa akalla kananan yara miliyan 20 ne a Najeriya ba sa zuwa makaranta wanda kuma hakan barazana ce ga Kasar.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar na jiya Laraba, bayan da shugaban kwamitin ilimin makarantun Firamare da Sakandire Usman Lawal Adamu mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya gabatar da rahoto akan lamarin, Akpabio ya ce rashin zuwan yaran makaranata ka iya sanyawa su zama ‘yan ta’adda anan gaba.
Shugaban majalisaar ya ce matukar ba a tashi tsaye an dauki matakin da ya dace akan lamarin ba, nan gaba yara za su fada ayyukan laifi.

Bayan gabatar da rahotan Sanatoci sama 20 ne suka tafka muhawara akan batun.

Akpabio ya ce karuwar yaran da ba su zuwa makaranta babban hadari ne ga sha’anin tsaron ƙasar.
Shima mataimakin shugaban majalisar Sanata Barau I Jibrin ya ce hakan babbar matsala ce da ya kamata a tashi tsaye domin magance ta.
Barau ya kara da cewa matsalar ba iya gwamnatin kadai ta tsaya ba, suma al’umma su na da tasu rawar da za su taka akan lamarin.