Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce babu gudu babu ja da baya akan ranar da aka sanya domin gudanar da zaben shugabannin Kananan hukumomin Jihar.

A wallafar da gwamnan yayi a shafinsa Facebook a jiya, bayan taron mika tuta ga ‘yan takarar kananan hukumomin 44, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, Abba ya ce za a gudanar da zaben ne a gobe Asabar bisa bin doka.

Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnatinsa da Hukumar zaɓe ta Jihar KANSIEC sun shirya tsaf domin gudanar da zaɓen tare da rantsar da waɗanda suka yi nasara.

Gwamnan Abba na wannaan kalami ne bayan wani umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar, ta bai’wa hukumar KANSIEC kan ta dakatar da gudanar da zaɓen a gobe Asabar.

Bayan hukuncin Babbar kotun ta tarayya, a yau Juma’a, kuma Babbar Kotun Jihar, ta bai’wa hukumar ta KANSIEC umarnin gudanar da zaben a gobe a Asabar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: