Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da kalaman da mai baiwa shugabanb Kasa shawara na musamman kan tsanin tsaro Malam Nuhu Rubadu yayi na cewa wasu daga cikin jami’an tsaron soji na taimakawa ‘yan ta’adda da makamai.

Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a haedkwatar da ke birnin tarayya Abuja, a yayin ganawa da manema labarai a jiya Alhamis.

Rundunar ta ce babu wani jami’inta da ke taimakawa ‘yan ta’addan da suka addabi Kasar.

Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan Kasar ta mallakar makamai ne ta hanyar sacewa da suke yi a lokacin da suka kai hari sansanonin sojin Kasar.

Janar Buba ya kara da cewa rikicin Kasar Libya da rashin zaman lafiya a yankin Sahel ya bayar da damar shigowa da makamai cikin Kasar nan, wanda hakan ya kara rura wutar ta’azzara tashe-tashen hankula da aikata ta’addaci a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: