Babban bankin Kasa na CBN ya musanta jita-jitar cewa za a daina karbar tsofaffin kudin Kasar na Naira 200, 500, 1000 a ranar 31 ga wata Disamban shekarar 2024 .

Mai magana da yawun bankin Hakama Sidi ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar ta ce har yanzu umarnin kotun koli na ci gaba da amfani da tsofaffin talkardun kudi da sabbin yana nan.

Hakama ta bayyana cewa har kawo yanzu bankin na CBN bai janye daga umarni daga bankuna da cibiyoyin hadahadar kudade na ci gaba da amfani da tsoffin kudin da aka sauyawa fasali ba.

Bankin ya kuma bukaci ‘yan Kasar da su yi watsi da jita-jitar wadda ba ta da tushe balle makama, kuma babu ranar daina amfani da tsoffin kudin.