Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a fadin Jihar daga Karfe 12:00 na dare zuwa karfe 6:00 na yammacin gobe Asabar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye ya fitar a yammacin yau Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin ta sanya dokar ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a Jihar.

Dantiye ya yi kira ga al’ummar Jihar, da su mutunta dokar wajen takaita zirga-zirga domin bayar da haɗin kai don ganin an gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin jihar cikin nasara, gaskiya da kuma adalci ga kowa.

Kwamishinan ya bayyana cewa dokar ta shafi dukkan Kananan hukumomin 44 na Jihar da mazabu 484 da ke fadin Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: