Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima ya yiwa wata ganawa da shugaba Bola Tinubu, tare da yi masa bayanin halin da Kasar ke ciki a lokacin da ya tafi hutun makonni biyu da ya tafi ketare.

Shettima ya kuma yi wa Tinubu bayani akan tafiyarsa zuwa ƙasar Sweden inda ya wakilci shugaban zuwa Kasar ta Sweden.
Kashim Shettima ya gana da shugaba Tinubu ne a ofishinsa a yau ranar.

Idan baku manta ba a ranar 2 ga watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya bar birnin tarayya Abuja zuwa ƙasar Birtaniya domin yin hutun makonni biyu.

Mai magana da yawun shugaban na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ne dai ya sanarwar da hutun da shugaban ya tafi.
Amma a ranar 19 ga watan Oktoba nan Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya bayan hutun makonni biyu a Burtaniya da Kasar Faransa.
Sai dai Kafin dawowar Shugaba Tinubu gida Najeriya, shima mataimakinsa Kashim Shettima ya tafi ziyarar kwanaki biyu a ƙasar ta Sweden.
Shugaban ya bukaci da mataimakin nasa Shettima da ya wakilci Najeriya a taron kasashen rainon Ingila wanda da aka gudanar a Samoa.
Sai dai Shettima bai samu damar halarta ba, bisa wata matsala da ta samu jirginsa a birnin New York.
Kashim Shettima ya dawo Najeriya yayin da tawagar ministocin ta halarci taron.