Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III, ya bayyana cewa batun Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta babban ƙalubale ne ga shugabannin yankin Arewacin Kasar.

Alhaji Sa’ad ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga ƙungiyar gwamnonin Arewa a wani taro da aka gudanar a Jihar Kaduna a yau Litinin.
Sarkin Musulmi ya ce akwai miliyoyin irin wadannan yara da suke yawo a garuruwa birane da ƙauyuka a fadin yankin.

Alhaji Sa’ad ya bukaci gwamnonin da su sanya batun a cikin tattaunawarsu ta koda yaushe, inda kuma ya jaddada bukatar magance matsalar a yankin.

Sarkin ya ce a matsayinsu na shugabanni za su goyi bayan kafa hukumar Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin na Arewa domin ganin an samu nasara akan lamarin.
Sarkin Musulmin ya kara da cewa Idan aka zagaya Jihohi, birane da kuma kauyuka, abin babu dadin gani, duba da yadda kananna yara ke gagaran ba akan tituna.
Ya ce kafa hukumar hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen matsalar a yankin da ake da kuma barazanar da yankin ke fuskanta.