Rundunar ƴan sandan Jihar Delta ta tabbatar da kama wani tsohon kansila a Jihar bisa zarginsa da hannu a yunkurin yin garkuwa da mutane.

Jami’an sun kama tsohon kansilan ne mai suna Mista Okechhukwu, a lokacin da suka same shi da hannu a yunkurin garkuwa da wata mata a ƙauyen Abbi da ke ƙaramar Ndokwa ta Yamma a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bright Edafe ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.

Kakakin ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan baturen ‘yan sandan yankin Abbi, Florence Onum, ta samu bayanan sirri kan cewa akwai shirin yin garkuwa da wata babbar mata a yankin.

Acewar kakakin jami’an ƴan sanda sun fara gudanar da binciken bayan samun bayanan sirrin, inda kuma a ranar 21 ga watan Oktoba nan da misalin ƙarfe 9:00 suka kama kansilan wanda ya fito daga ƙauyen Emu-Uno tare da wani mutum ɗaya.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa an dakatar da shi daga zama kansila a yankin, inda ya ce yana son yin garkuwa da matar ne domin ƙaramar hukumar ta biya kuɗin fansa inda ya ce ya san matar ta na kusa da shugaban karamar hukumar.

A halin yanzu dai kakakin ya ce wanda ake zargin yana tsare a hannunsu ana ci gaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: