Fadar shugaban Kasa ta musanta Jita-jitar da ake yadawa cewa shugaba Bola Tinubu ya nada kansa a matsayin minisan man fetur.

Mai magana da yawun shugaban na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata.

Onanuga ya kuma sake musanta jita-jitar ne a yayi shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi a lokacin da ya ke amsa tambayoyi.

Bayo ya ce ko kadan shugaban Tinubu bai taba samarwa da kansa wani mukamin minista ba a bangaren man fetur.

Bayo Onanuga ya kara da cewa Shugaban bai taba kiran kansa a matsayin ministan man fetur ba, shafukan sada zumunta ne suka nadashi a muƙamin Ministan.

Bayo ya bayyana cewa akwai ministoci biyu a ɓangaren man fetur, guda an ware shi ne a fannin harkokin iskar gas, kuma ɓangare ne mai muhimmanci da aka yi watsi da shi.

Acewarsa shugaba Tinubu na bunƙasa ɓangaren gas, inda ya yi nuni da kalaman tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, wanda ya ce ya yi kuskure a mulkinsa.

Sannan Onanuga ya musanta zarge-zargen da ƴan Kasar ke yi Shugaba Tinubu na cewa ba ya tausayayinsu bisa halin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta, inda ya ce Tinubu ya na sa ne ɗa wahalar da ake ciki a Kasar kuma ya mayar da hankali ne wajen warware dukkan kalubalen da ake fama da shi a Kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: