Rahotanni na nuni da cewar an sake samun karin farashin man fetur a jihar Legas jiya Talata

Mutane a jihar Legas sun wayi gari da ganin sabon farashin man fetur.

An siyar da man kan naira 1,025 kowacce lita maimakon naira 998 da ake siyarwa a karin da aka yi baya bayan nan.

Gidajen mai na NNPC ke siyar da mai naira 1,025 a Legas.

A babban birnin tarayya Abuja ma an siyar da lita guda naira 1,060 kowacce lita

Wannan na zuwa ne yayin da farashin gangar mai ta fadi a kasuwar duniya.

A baya kamfanin mai na NNPCL ya ce ya samu karin farashin mai da yake siyowa daga matatar mai ta Dangote.

Dalili kenan da ya sa shi ma ya ƙara farashinsa a gidajen man sa.

A cewar kamfanin, a halin yanzu kasuwa ce ke halinta, sai dai kuma farashin gangar mai sauka ya yi a wannan lokaci.

Idan za q iya tunawa a baya, mun baku labarin yadda mutane da dama su ka ajiye ababen hawansu sakamakon tsadar man fetur da ake fuskanta a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: