Shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya buƙaci ƴan kasuwa da kamfanin mai na NNPCL da kada su dinga shigo da mai daga waje.

Dangote ya ce matatarsa ta isa wadata Najeriya da man fetur din da ta ke buƙata.

Dangote ya bayyana haka ne a gaban kwamitin da aka samar kan siyarwa da matatarsa da sauran matatu danyen mai a kuɗin Naira.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci zaman wanda aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban ya yi bayani kan yadda siyar da man a kuɗin naira zai samar da ci gaba a ɓangaren.

A nasa bangaren, Dangote ya tabbatarwa da shugaban kasar cewaz za su dinga siyarwa da yan kasuwa mai lita miliyan 30 aa kowacce rana.

Sannan a shirye su ke domin fara aiwatar da hakan.

Haka kumq ya bukaci yan kasuwa da kamfanin mai mai zaman kansa na Najeriya NNPC da su dakatar tare da daina shigo da mai daga waje kwatakwata.

A kwanakin baya, kamfanin ya bayyana cewar matatar ta Dangin ta gaza cika alkawarin da ta dauka na samar da man da ta ce za ta dinga samarwa a kowacce rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: