Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugaban rundunar sojin ƙasa na riko.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da hadimin shugaban Bayo Onanuga ya fitar.
Shugaba Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatibosun a matsayin shugaban na riko.

Wannan na zuwa ne bayan dogon hutun da shugaban sojin Taoreed Labgaja ya tafi.

A baya an yi zargi tare da yada jita jitar cewar ya mutu.
Sai dai rundunar sojin ta fito ta musanta
Daga bisani ma helkwatar tsaro ta sake musanta batun.