Rahotanni sun nuna cewar lalacewar wutar lantarki da aka samu a jihohin arewacin Najeriya ƴan bindiga ne ke da alhakin hakan.

Wasu al’umma a jihar Neja sun ce an dade yan bindiga na kai hare-hare babban layin wutar Shiroro zuwa Kaduna.

Wani mai rike da sarautar gargajiya ya bayyana cewar, hanyar wutar waje ne da yan bindiga ke kai kawo, hakan ya sa zai yi wahala kafin a kai ga gyaran wutar

A cewarsa, ba za q iya tsayar da takaimaiman lokacin da za a iya gyaran wutar ba.

Sai dai ya ce an samu raguwar kai hare-hare, amma duk da haka wasu kutanen ba su koma gidajensu ba.

Basaraken da ke ƙaramar hukumar Munya, ya ce gyaran wutar na iya ɗaukar lokaci saboda yankin da wutar ta lalace waje ne da yan bindiga ke kai kawo.

Jihar Naija na daga cikin jihohin da ƴan bindiga su ka addaba da kai hare-hare tsawon lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: