Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta musanta rahotan da ake yaɗawa cewa ta tsare yara kanana masu zanga-zanga a gidan ajiya da gyaran hali na Kuje da ke birnin Tarayya Abuja.

Mai magana da yawun hukumar Abubakar Umar ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Kakakin ya ce a tsarin dokar hukumar jami’ansu ba su da hurumin tsare kananan yara a wajen da aka samar saboda manya.

Kakakin ya kara da cewa dokar ta kuma ba su damar kin karbar karin wasu mutane domin tsarewa, matukar an tabbata cewa gurin da za a ajiye su ya cika.

Hukumar ta ce babu kamshin gaskiya a jita-jitar da ake yadawa cewa an ajiye yaran a gidan gyaran hali na Kuje, inda ya ce a doka babu wani guri da aka kebance da za a ajiye yaran a gidan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: