Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta EFCC ta kama Akanta Janar na Jihar Edo Mr. Julius O. Anelu TARE da wasu manyan jami’an gwamnatun Jihar hudu bisa wasu zarge-zarge da ake yi musu.

Kamen da hukumar ta yiwa mutanen na zuwa ne kwanaki 11 kafin Gwamnan Jihar Godwin Obaseki ya miƙa mulkin Jihar ga zaɓaɓɓen gwamna Sanata Monday.
Wasu Rahotannin sun bayyana cewa jami’an EFCC sun tsare jami’an gwamnatin ne domin hana cire kuɗi daga lalitar gwamnatin Jihar Edo biyo bayan wani kasafi da ake zargin majalisar dokoki ta amince.

Wata majiya ta ce kama Akanta Janar da sauran mutane huɗun ne ya dakatar da dukkan ayyukan gwamnatin Jihar sakamakon su ne ka iya sa hannu a yayin cire kudi a asusun gwamnatin Jihar.

Majiyar ta ce lamarin ya haifar da cikas a harkokin gwamnatin Jihar domin a halin yanzu ba a iya biyan alawus-alawus na ma’aikata, ƴan fansho da sauransu.
Majiyar ta ce EFCC ta kudiri aniyar ci gaba da tsare jami’an da aka kama har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba nan a lokacin da wa’adin gwamnatin mai barin gado zai kare.