Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin gaggauta dawo da ƙananan yaran da aka gurfanar a gaban kotu a Abuja zuwa mahaifar su Kano.

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook a jiya.

A wallafar da gwamnan ya yi a shafin nasa, ya umarci Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Haruna Isa Dederi, da ya gaggauta yin dukkan abinda ya dace domin dawo da yaran gaban iyayensu.

Gwamman na wannan kalami ne bayan da aka gurfanar da yaran a gaban kotu domin yi musu hukunci, bisa zarginsu da ake yi da lalata kayan gwamnatin Kasar, da sauran wasu laifuka da ake tuhumarsu, a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a Kasar tun a ranar 1 ga watan Augustan shekarar nan.

Gurfanar da yaran masu kakannan shekaru a gaban kotu a Abuja, ya haifar da suka ga gwamnatin tarayya, da tare da yin Allah-wadai da matakin gurfanarwar da ta dauka akan yaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: